Najeriya

Sojojin Najeriya 380 za su ajiye kaki

Akalla sojojin Najeriya 380 ake sa ran su tube kakinsu nan da watanni 6 masu zuwa, a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen yaki da mayakan Boko Haram da kuma 'yan bindigar da suka addabi yankin arewacin kasar.

Wasu dakarun sojin Najeriya dake yakar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wasu dakarun sojin Najeriya dake yakar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar. REUTERS/Warren Strobel
Talla

Rahotanni sun ce wasu daga cikin wadannan sojoji 380 na sahun gaba cikin wadanda ake tinkaho da su wajen yaki da book haram da aka kwahse sama da shekaru 10 kasar na fafatawa, yayin da sauran kuma suka fito daga wasu sassa daban daban.

Jaridar Premium Times da ake wallafawa a kasar tace banda 356 da zasu bar aikin sojin saboda rashin gamsuwa, 24 daga cikin su za suyi ritaya ne domin karbar Sarautar Gargajiya a garuruwan su, abinda ya kawo adadin zuwa 380, kuma tuni shugaban rundunar sojin Janar Yusuf Tukur Buratai ya amince da bukatar su.

Ganin yadda matsalar tsaro ta addabi Najeriya musamman yaki da book haram da Yan bindigar da suka yiwa yankin arewa maso yammacin Najeriya illa, ya sa Majalisar dokokin kasar ta bukaci kara yawan sojojin da ake dauka domin karfafa musu gwuiwa da kuma tabbatar da kare lafiyar jama’a da dukiyoyin su.

Shugaban Majalisar Dattawan kasar Ahmed Lawal yace a shirye suke su amince da kasafin kudi na musamman daga bangaren zartarwa wanda zai bada damar kara yawan sojojin da kuma saya musu kayan aikin da suke bukata lokacin da suka gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI