Najeriya

Ma'aikatan agaji basa iya zuwa kananan hukumomi 9 a Borno - MDD

Ofishin kula da ayyukan jinkai na majalisar dinkin duniya, yace ma’aikatan agaji basa iya isa ga akalla kananan hukumomi 9 dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, sakamakon dakatar da ayyukan isar da kayayyakin agaji zuwa yankunan ta hanyar amfani da jirage masu saukar ungulu da majalisar dinkin duniyar ta yi.

Wasu jami'an agaji dake aiki a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya. 2/3/2018.
Wasu jami'an agaji dake aiki a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya. 2/3/2018. OCHA/Yasmina Guerda/File Photo/REUTERS
Talla

Lamarin dai ya auku ne a ranar 2 ga watan Yulin nan, lokacin da mayakan Boko Haram suka kai farmaki kan garin Damasak dake karamar hukumar Mobbar, inda suka halaka fararen hula 2, tare da kakkabo wani jirgin hukumar lura da ayyukan jinkan majalisar dinkin duniya.

A waccan lokacin dai rahotanni sun bayyana cewa jirgin bai fado ba, inda matukinsa ya yi gaggawar komawa cikin garin Maiduguri mai tazarar kilomita 150 daga inda farmakin ya faro, sai dai lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula biyu da kuma raunata wasu da dama.

Hukumar ayyukan jinkan tace kananan hukumomin da a yanzu ba a iya isa gare su a dalilin dakatar da ayyukanta sun hada Dikwa, Gamboru-Ngala, Kala Balge, Damboa, Mobbar, Bama, Gwoza, Kukawa, da kuma Munguno.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI