Najeriya ta gano hukuncin da ke neman ta biya P&ID diyyar dala biliyan 10
Gwamnatin Najeriya ta bankado wani hukuncin kotu da aka yanke akan ta wanda ya bukaci biyan makudan kudade saboda soke wata kwangilar iskar gas da aka bai wa kamfanin P&ID a shekarar 2010 da yanzu haka ake bukatar kasar ta biya Dala biliyan 10 ga kamfanin.
Wallafawa ranar:
Shi dai wannan kamfani na P&ID ya samu nasara a kotu ne dangane da kwangilar da ya samu a Najeriya da aka soke, wanda kotu ta umurci a biyan shi Dala biliyan 6 da rabi a matsayin diyya.
Rahotanni sun ce kudin ruwan da ke karuwa kan Dala biliyan 6 da rabin yanzu haka ya mayar da kudin da kamfanin ke bukata daga Najeriya zuwa Dala biliyan 10, abinda ya sa gwamnatin kasar ta ruga kotu domin samun mafita.
Rahotanni sun ce yanzu haka Najeriya ta bukaci kotu a Ingila da ya sake duba hukucin da ya yanke a shekarar 2017, duk da yake cewa kasar ta gaza daukaka kara cikin kwanaki 28 bayan yanke hukunci da ta yi.
Gwamnatin Najeriya ta gabatar da shaidar da ke nuna cewar ta biya kamfanin Dala 4,969.50 a ranar 30 ga watan Disambar shekarar 2009 da kuma Dala 5,000 ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2012.
Ana danganta wannan kamfanin na P&ID da wata ‘yar tsohon jami’in gwamnatin Najeriya da hukumar EFCC ta gurfanar a kotu akan zargin cin hanci da rashawa.
Takaddama tsakanin kamfanin P$ID da gwamnatin Najeriya ya yi kamari inda ake cigaba da fafatawa a kotu na.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu