Sojin Najeriya sun halaka kwamandojin Boko Haram a Borno
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar halaka wasu kwamandojin mayakan Boko Haram, yayin gumurzun da suka yi a jihar Borno.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar tsaron Najeriya ta ce, dakarun sojin sun kaiwa mayakan samame ne a kan iyakar najeriya da Kamaru, lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa dajin Sambisa.
Sanarwar tace sojin Najeriyar sun kuma yi nasarar kwace makamai, tarin alburusai, Mota da kuma kekuna.
Ma’aikatar tsaron Najeriya ta ce daga cikin manayan kwamandojin na Boko Haram akalla 8 da ta halaka akwai, Ba Issoufou da ake kira da Tumbun Dabino, Amir Batam/ Tumbun Bororo da kuma Koukar Kowa/Tumbun Dila.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu