Najeriya

Ni kadai ke da hurumin sauke hafsoshin tsaro-Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce shi kadai ke da hurumin nadawa ko sauke wani babban hafsan soji a mukaminsa, sabanin umurnin da Majalisar Dattawan kasar ta bayar da ke cewa, hafsoshin sojin su sauka ko kuma a sauke su daga mukamansu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugaban hafsan sojin kasa Janar Tukur Yusuf Buratai a Maiduguri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugaban hafsan sojin kasa Janar Tukur Yusuf Buratai a Maiduguri cfr
Talla

Sanarwar da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya rattaba wa hannu ta ce, shugaban ya ji matsayin da Majalisar Dattawan ta dauka a wannan Talatar, amma su san da sanin cewar, babu wanda yake da hurumin nada hafsan soji ko kuma sauke shi daga mukaminsa sai shi kadai.

Ita dai Majalisar Dattawa ta tafka mahawara kan tabarbarewar tsaro da kuma kashe sojojin kasar da 'yan bindiga suka yi a Jihar Katsina, inda 'yan majalisun suka nuna rashin amincewarsu da tabarbarewar al’amura a cikin kasar.

'Yan Majalisun sun yanke hukuncin bai wa hafsoshin sojin shawarar sauka daga mukamansu saboda gazawa, ko kuma a kore su daga bakin aiki.

'Yan Najeriya sun dade suna bayyana damuwa kan yadda harkokin tsaro ke tabarbarewa, lura da yadda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a cikin kasar baya ga rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI