Najeriya

Magu ya bayyana yadda ya yi rabon kadarorin da EFCC ta kwato

Dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya Ibrahim Magu ya yi ikirarin bai wa wasu daga cikin ma’aikatu da sassan gwamnati dama Majalisar kasar wani bangare na motoci da kadarorin da ya kwato daga hannun wadanda suka wawure dukiyar kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu Sahara Reporters
Talla

A bayanansa gaban kwamitin bincike Ibrahim Magu ya ce maimakon shigar da bayanan kadarorin da ya kwato ko kuma sanya kudin cikin asusun bai daya na gwamnatin kasar ya raba wani bangare na kudaden ga daidaikun mukarraban gwamnati da ma’aikatu.

A makon jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Magu inda tuni ya fara fuskantar tuhuma karkashin tawagar bincike ta musamman bisa jagorancin Ayo Salami tsohon shugaban kotun daukaka kara ta Najeriya.

Jaridar Premiums Times a Najeriyar ta ruwaito cewa bayan tarin tambayoyin da Magu ya amsa kan karkatar da kudade biyo bayan bukatar hakan daga ministan Shari’ar Najeriyar Abubakar Malami, Magun ya musanta batun arzurta kansa, yayinda ya fara bayyana yadda ya rabawa hatta wasu makusantan Buharin makudan kudade ciki har da shi kansa ministan shari’ar.

Ko da dai Jaridar ta Premium Times ta ruwaito Abubakar Malain na musanta batun arzurta kansa da dukiyar da Magun ya kwato ta cikin wata wasika da ya aikewa tawagar Ayo Salami.

Magu cikin amsoshin da ya bayyana ya ce rabon motoci 224 da ya yiwa wasu ma’aikatun kasar sun gudana ne bisa sahalewar shugaba Muhammadu Buhari.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI