Najeriya

PDP ta bukaci Buhari ya yi murabus saboda rashin tsaro

Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya sauka daga mukaminsa saboda yawan kashe-kashen da ake ci gaba da samu a kasar da kuma cin hanci da rashawar da suka dabaibaye harkokin gwamnatinsa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. © Nigeria Presidency
Talla

Jam’iyyar wadda ta bayyana haka a taron manema labarai ta ce, gwamnatin Buhari ta rude ta kuma rasa abin da za ta saka a gaba wajen yaki da Kungiyar Boko Haram da masu garkuwa da mutane da kuma 'yan bindigar da ke kashe jama’a ba  ji ba gani.

Shugaban Jam’iyyar Uche Secondus ya ce matsayin Majalisar Dattawa cewar shugabannin rundunonin sojin kasar su sauka daga mukamansu saboda gazawa wajen kare lafiyar jama’a, ya nuna cewar bangaren zartarwa ba ya aikin da ya rataya a kansa.

Secondus ya ce tun lokacin da Kungiyar Transparency International ta bayyana cewar cin hanci da rashawa mafi muni na faruwa ne a karkashin wannan gwamnati, matsalar sai ci gaba da karuwa ta ke yi, ganin yadda yanzu matsalar ta zama ado tsakanin jami’an gwamnati cikinsu har da hukumar da ke yaki da cin hancin.

Jam’iyyar PDPn ta yi gargadin cewar Najeriya ta kama hanyar fadawa cikin matsalar tattalin arziki kuma hakan na da nasaba da cin hancin da ke gudana a tsakanin jami’an gwamnati da ke rike da manyan mukamai.

Secondus ya ce abin takaici ne yadda ake sace kudaden da aka kwato daga hannun barayin gwamnati a gaban jama’a da kuma shugaban kasar da ke ikrarin yaki da cin hanci da rashawa.

Jam’iyyar ta ce abin da suke gani yau shi ne yadda Najeriya ta kama hanyar rugujewa saboda wadannan matsaloli da suka dabaibaye ta wanda ya zama wajibi shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayinsa na dattijo ya yi jifa da kwallon mangoro domin ya huta da kuda wajen sauka daga mukaminsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI