Najeriya

Dalilin da ya sa na koma APC bayan ficewa daga PDP - Dogara

Tsohon shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya bayyana dalilan da suka sa shi ya sake sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC bayan shugaban riko na Jam’iyyar Mai Mala Buni ya sanar da komawar sa cikin Jam’iyyar ta su.

Tsohon shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Yakubu Dogara
Tsohon shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Yakubu Dogara TWITTER/House of Representatives
Talla

A wasikar da ya rubutawa Jam’iyyar PDP a mazabar sa ta Bogoro, Dogara yace rugujewar shugabanci a Jihar sa ta Bauchi a karkashin gwamnatin Bala Muhammed da ya taimakawa samun nasara shine dalilin da ya sa ya bar Jam’iyyar.

Dogara yace ba zai iya bude baki yayi tambaya kan yadda ake tafiyar da gwamnatin Jihar ba sai a zarge shi da rashin biyayya, saboda haka ya haure takalman say a fice daga Jam’iyyar.

Tsohon shugaban Majalisar yace idan ya nade hannayen sa yaki cewa komai kan yadda al’amura ke tabarbarewa a Jihar Bauchi a karkashin gwamnatin Bala Muhammed zai zama maci amana, bayan a lokacin Gwamna Isa Yuguda da Mohammed Abubakar kowa ya ji muryar sa ya na bayyana ra’ayin sa idan yaga ba daidai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI