Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 10 a Suleja

A Najeriya Akalla mutane 10 cikinsu harda wata mai juna biyu da yaranta 4, sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta rutsa da su a garin Suleja dake jihar Niger, bayan saukar mamakon ruwan sama.

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane a Suleja dake Niger da kuma Gwagwalada dake Abujan Najeriya
Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane a Suleja dake Niger da kuma Gwagwalada dake Abujan Najeriya REUTERS/Tife Owolabi
Talla

Rahotanni sun ce ruwan sama ya soma sauka kamar da bakin kwarya ne tun misalin karfe 4 na asuba zuwa kusan 7 na safe, hakan ya haifar da ambaliyar ruwan da yayi awon gaba da wasu gidaje a Rafin-Sanyi, da kuma unguwar-Gwari dake wajen garin na Suleja.

Shaidun gani da ido sun ce akwai mutanen da har yanzu ba a kai ga gano su ko gawarwakinsu ba.

A wani labarin kuma  wasu mutane 5 sun mutu a Gwagwalada dake birnin tarayya Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI