Najeriya

Tubabbun 'yan Boko Haram za su fara hulda da jama'ar Borno

Wasu mayakan Boko Haram da aka kama a can baya a jihar Borno.
Wasu mayakan Boko Haram da aka kama a can baya a jihar Borno. REUTERS/Ahmed Kingimi

Mahukunta a Najeriya sun ce yanzu haka tubabbin ‘yan Boko Haram 602 ‘yan asalin jihar Borno na shirin komawa cikin al’umma, bayan sun kammala samun horo a game da sauya halaye da koyon sana’a-o’in hannu a wata cibiya da aka kafa a jihar Gombe.

Talla

Sai dai jama’a musamman a jihar ta Borno na ci gaba da nuna fargaba a game da batun sake dawo da tsoffin mayakan don rayuwa a cikin al’umma.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar tattaunawar da Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya yi da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Borno, Baba-Kura Abba-Jato, inda ya yi bayani game da tubabbun na Boko Haram.

Tubabbun 'yan Boko Haram za su fara hulda da jama'ar Borno

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.