Najeriya

Tsuntsaye sun lalata amfanin gona a sassan jihar Sokoto

Wasu tsuntsaye jan baki a gaf da tsaunin Kilimanjaro dake kasar Tanzania.
Wasu tsuntsaye jan baki a gaf da tsaunin Kilimanjaro dake kasar Tanzania. Lip Kee Yap/Flickr

Manoma a jihar Sokoto dake Najeriya, na kokawa kan yadda suke fuskantar matsalar tsuntsaye masu cinye albarkatun gona musamman Gero da shinkafa.Wannan matsala ta kunno kai ne a daidai lokacin da farashin kayan abinci ke hauhawa a Najeriya, abinda wasu ke alakantawa da matsalar tsaron dake hana manoma zuwa gonaki, da kuma matsin tattalin arzikin da annobar coronavirus ta haddasawa kasashen duniya.Wakilinmu Faruk Mohammad Yabo yayi nazarin yanayin da manoman ke ciki a yankin na Sakoto cikin rahoton da za a saurara.

Talla

Tsuntsaye sun farwa amfanin gona a sassan jihar Sokoto

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.