Najeriya

Gwamnan Borno ya tsallake rijiya da baya a harin Boko Haram

Gwamnan Jihar Borno da ke Najeriya, Babagana Umara Zulum ya tsallake rijiya da baya a wani harin kwanton-bauna da mayakan Boko Haram suka kaddamar.

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum tare da dogaransa.
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum tare da dogaransa. RFI Hausa
Talla

Daya daga cikin dogaran Zulum ya ce, an kai wa ayarin motocin gwamnnan harin ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga garin Baga, inda ya rarraba kayayyakin abinci ga ‘yan gudun hijirar da suka rasa muhallansu.

Dogarin ya ce, gwamna Zulum na cikin koshin lafiya.

Gwamnan dai yawan tafiye-tafiye zuwa sassan jihar Borno domin ziyartar ‘yan gudun hijira da kuma wuraren da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kai wa hari.

Ko a bara, sai da gwamnan ya tsallake rijiya da baya bayan harin da Boko haram ta kaddamar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI