Harin bama-bamai ya halaka akalla mutane 5 a Maiduguri
Fashewar wasu abubuwa har kashi 3 da ake zaton bama-bamai ne a cikin garin Maiduguri, yayi sanadin mutuwar akalla mutane 5, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Wallafawa ranar:
Lamarin dai ya auku ne a unguwar Custom, Gwange da kuma Mairi dake garin na Maidguri.
Zuwa lokacin wallafa wannan labara, ba a kai ga tantance wani irin abu aka yi amfani da shi wajen kai harin ba, wanda tawagar kwararru jami’an tsaron sashin kwance abubuwa masu fashewa ke bincike akai.
Rahotanni sun ce abin fashewa na farko ya fada ne kusa da wani kafinta ne da dansa, inda ya halaka su. A unguwar Gwange kuwa abin fashewar na 2 ya fada kan wani gida ne, inda ya halaka karamin yaro da kuma akuya, yayinda abin fashewar kashi na uku ya halaka mutane 2.
Bello Yaro Danbatta daya ne daga cikin jami’an agajin da suka kai dauki bayan farmakin, wanda yiwa wakilinmu Bilyaminu Yusuf Karin bayani.
Bello Yaro Danbatta daya daga cikin jami’an agaji a Maiduguri
Harin dai na zuwane a dai dai lokacin da Al’ummar Musuli ke shirin bukukuwan Babar Sallah.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu