Najeriya

Majalisa za ta binciki zargin karin badakalar biliyoyin kudade a hukumar NDDC

Zauren majalisar dattijan Najeriya.
Zauren majalisar dattijan Najeriya. Twitter/@NGRSenate

Rahotanni daga Najeriya sun ce majalisar dattijan kasar ta karbi sabon korafi kan zargin karin almundahanar biliyoyin kudade a hukumar raya yankin Niger Delta.

Talla

Bayanai daga majiya a majalisar dattijan sun ce sabon zargin almundahanar kudaden bashi da alaka da binciken batan naira biliyan 40 da ake yi hukumar ta NDDC.

Makwanni biyu da suka gabata ne, babban daraktan hukumar ta raya yankin Niger Delta Daniel Pondei ya suma a daidai lokacin da ake masa tambayoyi gaban kwamitin majalisar dokokin Najeriya, kan zarge-zargen karkatar da makudan kudade.

A baya bayan nan ne dai shugaban najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin gudanar da sahihin bincike kan tuhume-tuhumen rashawa da satar kudaden da ake yiwa wasu daga cikin shugabannin hukumomi a karkashin gwamnatinsa, wadanda yace sun ci amanar da ya basu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI