Najeriya

Ana yi wa gwamnati zagon kasa kan tsaro - Zulum

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum
Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum RFI Hausa / Ahmad Abba

Gwamnan jihar Borno Babagana Umar Zulum, ya jaddada cewar akwai wadanda suke yiwa gwamnati zagon kasa ga kokarinta na magance matsalolin tsaro, matsalar da gwamnan yace ba za ta bari a kawo karshen tayarda kayar baya a arewa maso gabashin Najeriya ba.

Talla

Farfesa Zulum ya bayyana haka ne a yau lahadi, bayan ganawa da gwamnonin Kebbi da Jigawa, Atkiu Bagudu da Badaru Abubakar a Maiduguri, wadanda suka kai masa ziyarar jaje, kan tsira daga farmakin Boko Haram da yayi, a lokacin da suka kaiwa tawagarsa hari a garin Baga.

Zulum ya bayyana halin da ya shiga a garin na Baga yayin farmakin mayakan na Boko Haram a matsayin tashin hankali.

Gwamnan jihar ta Borno yace tabbas barnar mayakan Boko Haram ta fi muni daga shekarar 2011 zuwa 2015, idan aka kwatanta da kokarin gwamnati mai ci daga 2015 zuwa yanzu, la’akari da cewar a waccan lokacin kimanin kananan hukumomi 22 ke karkashin ikon kungiyar ta Boko Haram, sai dai duk haka, akwai masu zagon kasa ga kokarin da ake, wanda yace dole shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya san da hakan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI