Najeriya

Buhari ya nesanta kansa da kalaman Mamman Daura kan tsarin karba karba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Mamman Daura
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Mamman Daura Daily Nigerian

Fadar gwamnatin Najeriya tace kalaman da Mamman Daura yayi kan neman watsi da tsarin karba karba wajen shugabancin kasar, yayi hannun riga da matsaya ko ra'ayin shugaba Najeriyar Muhammadu Buhari.

Talla

Cikin sanarwar da ya fitar, kakakin shugaban Najeriya malam Garba Shehu, yace matsayin Mamman Daura kan tsarin na karba karba ra'ayinsa ne da baya wakiltar gwamnati.

Yayin zantawa da kafar BBC, ne makusancin na shugaba Buhari ya ce tsarin karba karba a shugabancin Najeriya, bai amfani kasar da komai ba, dan haka kamata yayi daga yanzu a rika maida hankali wajen zabar shugaban da ya cancanta kawai, ba tare da la’akari da bangaren da ya fito ba.

Tuni dai bangarori da dama ciki har da kungiyoyin Ohanaeze Ndigbo da Afenifere suka maida raddin caccakar ra’ayin na Mamman Daura, da cewar babu abinda Hakan zai haifar illa rarrabuwar kai a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI