Masu zanga-zanga sun jikkata 'yan sandan Jamus 45
Wallafawa ranar:
Akalla ‘yan sandan Jamus 45 aka yiwa rotse a birnin Berlin, yayin arrangama da masu zanga-zangar adawa da matakan hana mutane walwala saboda annobar coronavirus.
Jami’an tsaron Jamus sun ce yawan masu zanga-zangar da suka fita a ya kai dubu 20, sai dai wadanda suka shirya zanga-zangar sun ce adadin ya haura mutane dubu 300.
Mafi akasarin masu zanga-zangar dai na kallon barkewar annobar coronavirus a matsayin wani shiryayyen al’amari.
A halin da ake ciki ‘yan sandan na Jamus sun kama mutane 133 daga cikin masu zanga-zangar.
Kamfanin dillancin labarai na AFP yace kalilan daga masu zanga-zangar ne suka sanya takunkuman rufe baki da hanci, da kuma kiyaye bada tazara.
Hakan ta sanya ‘yan sandan na Jamus shigar da karar wadanda ke jagorantar zanga-zangar gaba kotu, bisa tuhumarsu da gazawa wajen tabbatar da bin dokokin kiyaye lafiyar jama’a yayin gangamin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu