Najeriya

Abinda ya faru ga Zulum a Baga alama ce ta muma bamu tsira ba - Gwamnoni

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce farmakin da gungun maharan da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kaiwa tawagar gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum a garin Baga, alama ce dake nuna cewar su kansu gwamnoni basu tsira daga barazanar kungiyar ta Boko Haram ba.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi
Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi The Guardian Nigeria
Talla

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriyar kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ne ya fitar da sanarwar hadin gwiwar ga manema labarai, bayan taron da suka yi a ranar litinin a Abuja.

Taron gwamnonin da ya maida hankali kan sha’anin tsaro, ya koka kan yadda lamurra ke kara tabarbarewa a sassan Najeriya, duk da kokarin gwamnati na kawo karshen matsalar.

Ranar lahadin nan da ta gabata yayin karbar bakuncin gwamnonin Jigawa da Kebbi a Maiduguri, gwamna Babagana Zulum ya jadadda cewar, akwai wadanda ke yiwa gwamnati zagon kasa ga kokarinta na murkushe ta’addanci, matsalar da yace ba za ta bari a kawo karshen matsalar da yankin arewa maso gabshin kasar ke ciki ba.

A wani labarin kuma mai alaka da wannan, yau Talata 4, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da manyan hafsoshin tsaron kasar da sauran masu ruwa da tsaki a Abuja, taron da ake kyautata zaton ya tattauna ne kan irin koma bayan da ake samu ga kokarin kawo karshen matsalolin tsaro a Najeriyar, la’akari da abinda ya faru da gwamnan Borno a garin Baga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI