Bakonmu a Yau

Injiniya Muhammad Tukur kan shirin kamfanin jiragen saman Air Peace na sallamar matukansa sama da 70

Sauti 03:14
Jirgin saman kamfanin Air Peace kirar Boeing 777-300 a filin jiragen saman birnin Legas.  11/9/2019
Jirgin saman kamfanin Air Peace kirar Boeing 777-300 a filin jiragen saman birnin Legas. 11/9/2019 REUTERS

Katafaren kamfanin jiragen saman Air Peace dake Najeriya ya bayyana shirin sallamar matuka jiragen sa sama da 70 saboda kin amincewa da shirin rage musu albashi sakamakon illar annobar coronavirus.

Talla

Matukan sun sa kafa sun shure tayin rage albashin da kamfanin ya musu, inda suka ce gara su ajiye aikin su akai.

Dangane da wannan dambarwa Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar jiragen sama Injiniya Muhammad Tukur.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.