Najeriya

Manyan jami'an NDDC sun kashe kusan naira biliyan 5 kan kula da lafiya - Rahoto

Babban daraktan hukumar raya yankin Niger Delta Daniel Pondei bayan farfadowa daga suman da yayi, lokacin amsa tambayoyi gaban kwamitin majalisar dokokin Najeriya
Babban daraktan hukumar raya yankin Niger Delta Daniel Pondei bayan farfadowa daga suman da yayi, lokacin amsa tambayoyi gaban kwamitin majalisar dokokin Najeriya Daily Trust

Rahoton binciken da majalisar dattijan Najeriya ta fitar kan almundahanar biliyoyin kudade a hukumar raya yankin Niger Delta NDDC, ya bankado cewar, manyan jami’an hukumar sun raba naira biliyan 4 da miliyan 900 a tsakaninsu da sunan kudaden alawus na kula da lafiya.

Talla

Binciken majalisar ya kuma bankado cewar manyan jami’an na hukumar ta NDDC sun biya naira miliyan 114 da dubu 900 ga karin ma’aikatansu 26, duk a matsayin alawus na kula da lafiya, a tsakanin watan Maris da Afrilu, lokacin da annobar coronavirus ta tilasta rufe ma’aikatu, makarantu da kasuwanni, bayan kafa dokar hana zirga-zirga domin dakile yaduwar cutar.

Rahoton majalisar ya nuna cewar babban daraktan hukumar ta NDDC Daniel Pondei da kuma wasu manyan daraktoci 2 dake biye masa kadai, sun samu kason naira miliyan 14 da dubu 200 da kowanne ya zuba a aljihunsa.

Makwanni biyu da suka gabata ne, babban daraktan hukumar ta raya yankin Niger Delta NDDC Daniel Pondei ya suma a daidai lokacin da ake masa tambayoyi gaban kwamitin majalisar dokokin Najeriya, kan zarge-zargen karkatar da makudan kudade.

A baya bayan nan rahotanni suka ce majalisar dattijan kasar ta karbi sabon korafi kan zargin karin almundahanar biliyoyin kudade a hukumar ta NDDC.

Bayanai daga majiya a majalisar dattijan sun ce sabon zargin almundahanar kudaden bashi da alaka da binciken batan naira biliyan 40 da ake yi hukumar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI