Faduwar darajar Naira ta haifar tsadar rayuwa a Najeriya

Sauti 09:56
Kayayyakin masurufi sunyi tashin gauron zabi a Najeriya
Kayayyakin masurufi sunyi tashin gauron zabi a Najeriya financialtribune

Shirin Kasuwa Akai miki Dole na wannan makon ya duba kasuwar musayar kudin kasa da kasa ne a Tarayyar Najeriya, inda kudin kasar na Naira ke cigaba da faduwa, yayin da kimar kudaden kasashe ketare ke tashin gwaron-zabi. Wannan faduwar na darajar kudin Naira a cewar masana, na cigaba da haddasa mummunan tasiri a tattalin arzikin kasar, tare da haifar hauhawan farashin kayayyakin masarufi.