Najeriya

Jami'an tsaron Najeriya sun tarwatsa zanga-zangar #RevolutionNow

Jami'an tsaro lokacin kame masu zanga-zanga karkashin jagorancin Omoyele Sowore a Abuja
Jami'an tsaro lokacin kame masu zanga-zanga karkashin jagorancin Omoyele Sowore a Abuja Daily Post

Rahotanni daga Abuja da wasu birane a Najeriya, sun ce hadin gwiwar jami’an tsaro na ‘yan sanda da sojoji sun kama akalla mutane 60 daga cikin masu zanga-zangar neman sauyi ta #RevolutionNow.

Talla

Zanga-zangar ta ranar Laraba ta gudana ne a Abuja da wasu biranen Najeriya, a matsayin gangamin cika shekara 1 da kaddamar da zanga-zangar a ranar 5 ga watan Agustan shekarar 2019, a karkashin jagorancin tsohon dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar adawa ta AAC, Sowore Omoyele.

Kuna iya latsa alamar sauti dake kasa don sauraron rahoto daga wakilin mu na Abuja Mohammed Sani Abubakar.

Jami'an tsaro sun kama gwamman masu zanga-zangar #RevolutionNow a Abuja

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.