Najeriya

An kashe mutane 33 a Zangon-Kataf a Kaduna

'Yan sanda sun ce, mutane 21 suka rasa rayukansu a farmakin na Kudancin Kaduna.
'Yan sanda sun ce, mutane 21 suka rasa rayukansu a farmakin na Kudancin Kaduna. Jakarta Globe

A kalla mutane 33 sun rasa rayukansu akasarinsu mata da kananan yara bayan wasu ‘yan bindiga sun kai sabon farmaki a kauyukan yankin Atyap da ke Karamar Hukumar Zangon-Kataf ta jihar Kadunan Najeriya.

Talla

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta rawaito cewa, an kaddamar da jerin hare-haren ne da misalin karfe 11 na dare a ranar Laraba da kuma karfe 1 na dare a ranar Alhamis a kauyukan Apyiashyim da Atak’mawai da Kibori da Kurmin Masara da ke karkashin masarautar Atyap a Zangon Kataf.

Wata majiya ta bayyana cewa, an kai farmakin ne a daidai lokacin da ake tafka ruwan sama mai karfin gaske, yayin da tsagerun suka karkashe jama'a tare da raunata wasu da dama duk da cewa akwai dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24.

Daya daga cikin mazauna yankin ya ce, an kai musu farmakin ne a daidai lokacin da al’umma ke barci a gidajensu.

‘Yan bindigar sun shafe tsawon lokaci suna harbi kan mai uwa da wabi, yayin da majiyar rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ke cewa, mutane 21 ne suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI