Jonathan ya gargadi 'yan siyasa kan tashin hankali

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Daily Trust

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gargadi 'Yan siyasar kasar da su kaucewa duk wani yunkurin da zai haifar da tashin hankali, yayin da ya roke su da su rungumi hanyar inganta zaman lafiya da cigaban kasa.

Talla

Jonathan dake jawabi ga taron shugabannin Yan kabilar sa ta Ijaw yace ya zama wajibi Yan siyasa su sanya cigaban kasa a gaba, domin kuwa abinda siyasa ke bukata kenan amma ba raba kan jama’a ko kuma yaki da abokan gaba ba.

Tsohon shugaban yace a matsayin sa na mai fafutukar ganin dimokiradiya da shugabanci na gari ya wanzu a Najeriya da Afirka, bukatar sa itace ganin jama’ar sa sun taka gagarumar rawa wajen zabin wanda zai jagoran ce su da kuma yadda ake jagorancin.

Jonathan yace babu abinda dake mayar da al’umma ko kasa baya da ya wuce tashin hankali da kuma rikicin shugabanci, inda ya kara da cewar babu yadda za suyi ikrarin son jama’ar su a daidai lokacin da suke amfani da damar domin cimma biyan bukatun kan su.

Tsohon shugaban ya bukaci hadin kan jama’ar Najeriya da kuma kaunar juna wajen kulla kawance daga kowanne sashe domin fuskantar kalubalen da suka addabi jama’a a wannan lokaci.

Jonathan yace ya zama wajibi Yan Najeriya su fahimci cewar makomar kasar da nasarar ta ya dogara ne ga hadin kan kasa daga matakai daban daban.

Tsohon shugaban ya kalubalanci shugabannin Yan kabilar sa ta Ijaw da su kulla kawance da sauran kabilun Najeriya domin cimma muradun su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI