Najeriya

Boko Haram ta kashe sojoji da 'yan sanda

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau tare da mayakansa
Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau tare da mayakansa AFP PHOTO / BOKO HARAM

Mayakan Boko Haram sun hallaka fararen hula 223 da sojoji 82 da kuma 'yan sanda 7 a watanni 7 da suka gabata a Najeriya, yayin da kungiyar ke zafafa kai hare-hare.

Talla

Wani bincike da Jaridar Daily Trust ta gudanar ya ce, tsakanin 2 ga watan Janairu zuwa 2 ga watan Agustan bana, mayakan suka kashe wadannan mutane a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Ko makwanni biyu da suka wuce, gwamnan Borno Babagana umara Zulum ya tsallake rijiya da baya sakamakon irin wannan harin, abin da ya sa gwamnonin Arewa Maso Gabas suka gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ganin an sake dabarun kawo karshen wannan matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI