Bakonmu a Yau

Hira da Alhaji Isa Tafida Mafindi, dangane da hukuncin tara kan masu fashin Teku.

Sauti 03:39
Masu fashin taku a gaban ruwan Guinea
Masu fashin taku a gaban ruwan Guinea AFP PHOTO / MOHAMED DAHIR

A karon farko a Najeriya, wata kotu ta zartas da hukunci kan masu fashin jiragen kan teku, al’amarinda zai nuna azahiri kasar da gaske take yi game da sauye-sauye ta fannin yawaitan fashi a teku.

Talla

Kotun dake zama a Port Hacourt ta ci taran kudi Naira miliyan 10 kan kowannensu saboda laifin fashin jirgin ruwa a watan uku na wannan shekaran, inda suka karbi kudin fansa na dalar Amurka dubu 200 don sakin matuka jirgin ruwan.

Dangane da wannan hukunci Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Alhaji Isa Tafida Mafindi Masani gameda sha'anin jiragen ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.