Amnesty ta bukaci watsi da hukuncin kisa kan mawakin Kano

Kungiyar Amnesty International ta bukaci Hukumomin Jihar Kano dake Najeriya da suyi watsi da hukuncin kisan da aka yankewa Yahaya Aminu Sharif da kotun Islama ta samu da laifin batunci ga Manzon tsira Annabi Muhammad wanda tsira da amincin Allah suka tabbata a gare shi.

Yadda Kungiyar Amnesty ta gudanar da gangamin hana zartar da hukuncin kisa a Thailand
Yadda Kungiyar Amnesty ta gudanar da gangamin hana zartar da hukuncin kisa a Thailand ROMEO GACAD / AFP
Talla

Daraktan kungiyar a Najeriya Osai Ojigbo ta bayyana hukuncin a matsayin karan tsaye ga bangaren shari’a inda take cewa akwai shakku sosai dangane da yadda aka yiwa matashin shari’a da kuma yadda aka shirya tuhumar da aka masa.

Ojigbo tace rashin adalchin da aka nunawa Sharif wajen shari’ar ya sabawa ‘yancin rayuwa inda ta bukaci gaggauta sakin sa ba tare da gindaya sharidodi ba.

Amnesty tace hukuncin kisa ya sabawa hakkokin Najeriya a karkashin yarjejeniyar duniya wadda ta hana aiwatar da hukuncin ga wasu laifuffuka na daban da suka sabawa aikata kisa.

Idan dai ba’a manta ba wata kotun Musulunchi ta samu matashin mai shekaru 22 da laifin cin zarafin Manzan Allah Annabi Muhammad SAW inda ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI