Buhari ya kira manyan kasashen duniya da su saidawa Najeriya makamai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin jawabi gaban Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin jawabi gaban Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Carlo Allegri

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi kira ga kasashen duniya da su sakar da maran saidawa kasar Makamai da dangoginsa domin taimakata kawar da rashin tsaro dake addabarta yanzu haka.

Talla

Ministan yada labarai da al'adu na Najeriya Lai Mohammed, ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, yana mai cewa manyan kasashen na duniya su daina kafa hujjoji ta batutuwa da basu taka kara sun karya ba wajen hanawa kasar cinikin makamai.

Dangane da wannan bukata na gwamnatin Buhari a dai-dai wannan lokaci, munji ta bakin Malam Husaini Monguno masanin harkokin tsaro a Najeriya, kuma kuna iya latsa alamar sauti dake katsa domin sauraron abin da yake cewa.

Buhari ya kira manyan kasashen duniya da su saidawa Najeriya makamai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.