MBC taci taran gidan Radiyo Naira miliyan 5 saboda bidiyon Mailafiya

Masanin tattalin arziki a Najeriya Obadiah Mailafiya
Masanin tattalin arziki a Najeriya Obadiah Mailafiya .png

Hukumar Sadarwar Najeriya dake Kula da yadda kafofin yada labarai ke aiki ta NBC, taci tarar tashar rediyon ‘Nigeria Info’ naira miliyan 5 saboda yada labaran batanci dake iya tada hankalin jama’ar kasa.

Talla

Sanarwar da hukumar ta gabatar yace anyi amfani da tashar wajen yada labaran da basu da tushe ballantana makama kuma suna iya haifar da tashin hankali da aikata laifuffuka.

Hukumar ta bayyana damuwa kan abinda ta kira rashin kwarewa da kuma kaucewa ka’idar aiki da tashar Nigeria info ta nuna wajen baiwa tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya Dr Obadiah Mailafia damar amfani da tashar wajen kalaman dake iya tada hankalin jama’a.

Sanarwar Hukumar yace ya kamata kafofin yada labarai su san cewar, an basu lasisin aiki ne a matsayin amanar jama’a, saboda haka babu wata tashar da take da hurumin bada dama wajen yada kalaman da zasu iya haifar da tashin hankali.

Idan dai ba’a manta ba, Dr Mailafia a hirar da yayi da tashar yayi zargin cewar wasu shugabannin arewacin Najeriya na da hannu wajen tashe tashen hankulan da ake samu, inda ya bayyana cewar akwai wani tubabben dan kungiyar Boko Haram da ya bayyana cewar wani Gwamnan arewacin kasar na daga cikin shugabannin su.

Hukumar sadarwar tace ba zata yi kasa a gwuiwa ba wajen rufe duk wata tashar da ake amfani da ita wajen tada hankali ko kuma raba kan jama’ar kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.