Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Farfesa Umar Pate kan zargin da Mailafiya ya yi dangane da tsaro

Sauti 03:54
Dakta Obadiah Mailafiya masanin tattalin arziki a Najeriya
Dakta Obadiah Mailafiya masanin tattalin arziki a Najeriya .png

Sakamakon zargin da wani tsohon Mukaddashin Gwamnan Babban Bankin Najeriya Dakta Obadiah Mailafiya ya yi cewa wani Gwamnan arewacin kasar shine Kwamandan kungiyar Boko Haram, Gwamnonin arewa sun bukaci jamian tsaron kasar da su gudanar da cikakken bincike kan wannan zargi.

Talla

To sai dai kuma Alhamis din nan, Hukumar Kula da kafofin sadarwa ta kasar ta sanar da cin taran kudi Naira Biliyan biyar kan wani gidan Radio dake Lagos saboda yada zargin na Dakta Mailafiya.

Dangane da wannan batu ne, Mahamman Salissou Hamissou ya tuntubi Kaigaman Adamawa, Farfesa Umar Pate, Malami a sashin koyon aiki jarida a Jami'ar Bayero dake Kano don jin yadda suke kallon wannan dambarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.