Tsohon sarki Sanusi na II zai fara koyarwa a Oxford

Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II
Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II AFP

Jami'ar Oxford dake Birtaniya ta tabbatar da matsayin baiwa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanudi na II damar zama malami a cikin ta wanda zai fara aiki daga watan Oktoba mai zuwa.

Talla

Sanarwar da jami’ar ta gabatar ya nuna cewar Tsohon Sarkin zai yi aiki ne a Sashen dake nazarin tarihin Afirka da kuma kwalejin Anthony dake cikin makarantar.

Sanarwar tace tuni kwamitin gudanarwar Jami’ar ya amince da bukatar Mai Martaba Tsohon sarkin na bada gudumawa a kakar karatu mai zuwa na shekarar 2020 zuwa 2021.

Jami’ar tace Sarki Sanusi mai murabus zai yi amfani da wannan dama waje rubuta littafi akan ‘yadda Babban Banki ya taka rawa wajen matsalar tattakin arzikin duniya wanda zai mayar da hankali kan Babban Bankin Najeriya tsakanin shekarar 2009 zuwa 2013.

Jami’ar tace binciken zai baiwa Sarkin damar gabatar da kwarewar da ya samu lokacin da ya jagoranci Babban Bankin Najeriya a matsayin sa na Gwamna da kuma Masani.

Tsohon Sarkin ya jagoranci Babban Bankin Najeriya tsakanin shekarar 2009 zuwa 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.