'Yan bindiga sun kashe mutane 14 a Neja

'Yan bindiga a Najeriya
'Yan bindiga a Najeriya Daily Post

'Yan sanda a Najeriya sun ce wasu 'Yan bindiga dauke da makamai daban daban sun kai hari kauyen Ukuru dake karamar Hukumar Mariga a Jihar Niger, inda suka kashe mutane 14.

Talla

Mai Magana da yawun rundunar Yan Sandan Jihar Wasiu Abiodun yace Yan bindigar sun kai harin ne da rana inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, kana daga bisani suka sace musu shanu.

Bayan harin an tabbatar da mutuwar mutane 14, yayin da wasu kuma da suka samu raunuka aka kai su asibitin Mariga domin kula da su.

Jihar Niger na daga cikin Jihohin Arewa Maso Yamma da suke fama da matsalar tsaro, musamman Yan bindiga barayin shanu da kuma masu garkuwa da mutane domin karbar diyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.