An yi wa Kanawa gargadi kan ambaliyar ruwa
Wallafawa ranar:
Hukumar Agajin Gaggawa a Najeriya ta gargadi mazauna kananan hukumomi 20 daga cikin 44 da ke Jihar Kano da su yi shirin fuskantar ambaliyar ruwa sakamakon ruwan saman da ake samu a jihar akai akai.
Shugaban Hukumar da ke Kula da shiyar Kano Sanusi Ado ya shaida wa wani taron masu ruwa da tsaki a Kano cewar, ganin yadda ake samun ruwan, yana da matukar muhimmanci jama’ar wadannan kananan hukumomi su yi taka-tsan-tsan.
Daga cikin kananan hukumomin da ke fuskantar baraznar akwai Taruni da Gaya da Gezawa da Gwarzo da Ungoggo da Wudil da Nasarawa da kura da kuma birnin Kano.
Ambaliyar ruwa ta yi barna a wasu yankunan arewacin Najeriya a bana, inda ta lalata gidaje da albarkatun gona, yayin da ta yi awon gaba da dabbobi baya ga asarar rayuka da ake samu wani lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu