Ireland

Ireland za ta bai wa Najeriya Euro miliyan 5 daga kudin Abacha

Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soji, Janar Sani Abacha.
Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soji, Janar Sani Abacha. Issoug Sanogo/AFP/Getty Images

Gwamnatin Kasar Ireland ta sanya hannu kan yarjejeniyar mayar wa da gwamnatin Najeriya Euro miliyan 5 da rabi daga cikin kudin da tsohon shugaban kasar Janar Sani Abacha ya ajiye a cikin asusun bankin ajiyar kasar.

Talla

Ministar Shari’ar Ireland Helen McEntee ta ce shirin mayar wa Najeriya kudaden ya biyo bayan hukuncin kotu wadda ta bada umurnin yin haka a shekarar 2015.

McEntee ta bayayana cewar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar ta rufe asusun ajiyar a shekarar 2014, bayan da wasu lauyoyi daga Najeriya da ke wakilatn gwamnatin kasar suka tintibi gwamnatin Ireland.

Wannan sanarwa ta kawo karshen dogon lokacin da aka dauka wanda ya kunshi binciken kasashen duniya dangane da rufe asusun ajiyar tsohon shugaban kasar da ke kunshe da kudin da ya zarce sama da Dala biliyan guda, kuma Euro miliyan 5 da rabi na aje ne a kasar ta Ireland.

Mayar wa Najeriya da wadanan kudade zai zama irinsa na farko da gwamnatin Ireland ta yi a karkashin yarjejeniyar kasashen duniya a yunkurin yaki da cin hanci da rashawa da kuma masu halarta kudaden haramun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.