Najeriya

Dole a binciki zargin alakar daya daga cikinmu da Boko Haram - Gwamnoni

Wasu daga cikin gwamnonin arewacin Najeriya
Wasu daga cikin gwamnonin arewacin Najeriya Twitter/@@NTANewsNow

Gwamnonin Arewacin Najeriya sun sake bayyana matsayin su cewar ya zama dole ga jami’an tsaro su gudanar da bincike kan ikrarin tsohon mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Dakta Obadiah Mailafia cewar daya daga cikin su Kwamanda ne a kungiyar Boko Haram.

Talla

Daraktan yada labaran Gwamnan Jihar Plateau, Simon Lalong wanda ke shugabancin kungiyar, Makut Simon Macham yace suna bukatar ganin an gudanar da bincike kan zargin cewar, lokacin da aka killace mutane a kasa domin yaki da annobar korona, mayakan na raba makamai da kuma yawo ko ina a fadin Najeriya tare da amfani da jiragen su ba tare da bin doka hana zirga zirga ba.

Gwamnonin sun bayyana zargin Dakta Mailafian a matsayin mai girma wand aba za’a iya watsi da shi ba, saboda haka suke bukatar jami’an tsaro su tabbatar da gudanar da sahihin bincike kan lamarin domin gano gaskiyar sa.

Sanarwar tace su Gwamnonin arewacin Najeriya sun dade suna gudanar da tarurruka da kuma Allah wadai da yadda kungiyar Boko Haram da Yan bindiga ke hallaka jama’a tare da masu garkuwa da mutane, da zummar ganin an shawo kan matsalar, dan haka bayyana cewar wani daga cikinsu na daya daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram zargi ne mai girma da ba za su lamunce shi ba.

Ita ma Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bayyana takaici dangane da ikrarin Dakta Mailafia wanda tace ya bayyana nadamar sa akai, ya kuma nemi gafara lokacin da ya gurfana a gaban jami’an ta, amma kuma daga bisani ya sauya matsayin sa a gaban jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.