Najeriya

Za mu matsawa Buhari kan bukatar korar hafsoshin tsaro - Majalisa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin wani taro da manyan hafsoshin tsaron kasar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayin wani taro da manyan hafsoshin tsaron kasar Daily Trust

Majalisar Dattijan Najeriya tace za ta matsawa shugaba Muhammadu Buhari, wajen ganin ya kori manyan hafsoshin tsaron kasar, saboda gazawarsu wajen kawo karshen matsalar tsaron dake girmama a sassan Najeriyar.

Talla

Kafin shan wannan alwashi dai, a ranar 21 ga watan Yuli, majalisar dattiojan ta bukaci dukkanin hafsoshin rundunonin tsaron Najeriyar da su yi murabus, amma fadar gwamnati ta maida musu raddin cewar, shugaba kasar kadai ke da hurumin sauke su.

Wasu daga cikin dalilan da suka sanya zauren majalisar dattijan goyon bayan kudurin da sanata Ali Ndume ya gabatar, sun hada da farmakin baya bayan nan da mayakan Boko Haram suka kaiwa sojin Najeriya a kan hanyar damboa zuwa Maiduguri, inda suka halaka dakaru 24, tare da jikkata wasu akalla 19 a watan Yuli.

A baya bayan nan kuma, sama da sojoji 236 suka yi murabus bisa radin kansu, abinda wasu ke kallo matsayin gagarumin koma baya ga rundunar sojin Najeriya dake fuskantar kalubalen tsaro a sassan kasar.

Sai kuma a jihar Katsina, inda ‘yan bindiga suka yiwa sojojin kwanton bauna tare da halaka akalla 20, a dai watan Yulin da ya gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.