Najeriya

Gwamnan Borno na sanyaya gwiwar dakarunmu dake yakar ta'addanci - Sojoji

Wasu daga cikin sojojin Najeriya yayin atasaye a dajin Sambisa
Wasu daga cikin sojojin Najeriya yayin atasaye a dajin Sambisa YouTube

Rundunar sojin Najeriya ta zargi Gwamnan Borno Babagana Zulum da sanyaya gwiwar dakarunta dake yakar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, ta hanyar tuhumarta da zarge-zarge marasa tushe.

Talla

A watan da ya gabata, Gwamna Zulum ya caccaki sojojin, tare da tuhumarsu da kaiwa tawagarsa farmaki yayin ziyara a garin Baga, harin da a baya aka kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kai.

Yayin bayyana bacin ransa kan lamarin, gwamnan jihar ta Borno yayi barazanar hada rundunar mafarauta don baiwa garein na Baga tsaro, idan har sojoji suka gaza.

Sai dai bayan kammala bincike, manjo Janar Felix Omoigui, mataimakin babban kwamandan 'Operation Lafiya Dole', yace babu gaskiya a zargin da gwamna Zulum ke musu, kuma kalaman gwamnan na sanyaya gwiwar dakarunsu dake kokarin fatattakar kungiyar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.