Kano-Najeriya

Kano ta zama ta biyu a jerin jihohi masu yawan marasa aikin yi a Najeriya

Wasu matasa yayin jiran kada kuri'a a wata rumfar zabe dake jihar Kano. 28/3/2015
Wasu matasa yayin jiran kada kuri'a a wata rumfar zabe dake jihar Kano. 28/3/2015 REUTERS/Goran Tomasevic

Hukumar kididdig ta Najeriya NBS ta sanar da samun karuwar marasa aikin yi daga kashi 23.1 zuwa kashi 27.1 a watanni 6 na farkon shekarar nan.

Talla

Bayanan da hukumar ta fitar ya nuna cewa yanzu haka Kano ke matsayin ta biyu a jerin jihohin da ke da yawan marasa aikin yi a Najeriya wadanda galibin shekarunsu ya fara daga 15 zuwa 60 .

Alkaluman hukumar kididdigar sun nuna cewa jihar ta Kano da ke arewacin Najeriyar na da jumullar mutum miliyan 1 da dubu dari 4 da 20 galibinsu matasa da basu da aikin yi.

Yanzu haka dai Najeriyar na da alkaluman mutum miliyan 21 da dubu 764 da 617 wadanda basu da aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.