COVID-19: Najeriya ta tsayar da ranar bude iyakokinta na sama

Filin jiragen saman Najeriya na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Filin jiragen saman Najeriya na Nnamdi Azikiwe dake Abuja. Reuters/Albert Gea

Gwamnatin Najeriya ta bayyana 29 ga watan Agusta a matsayin ranar da za ta bada damar cigaba da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa zuwa ciki da wajen kasar.

Talla

Ministan sufurin jiragen saman Najeriya Hadi Sirika ya bayyana shirin sake bude iyakokin na sama ga kasashen ketare, yayin taron kwamitin yakar annobar coronavirus a Abuja.

Sirika ya bayyana cewar zirga-zirgar jiragen saman na kasa da kasa za ta soma ne daga filayen jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja da kuma na Murtala Muhammad a Legas.

Matakin sake bude iyakokin saman Najeriya, na zuwa ne a daidai lokacin da yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus ya kai dubu 49 da 485, bayan samun karin mutane 417 da suka kamu da cutar a tsakanin jihohi 16.

Sai dai zuwa yanzu mutane dubu 36 da 834 sun warke daga cikin kusan dubu 50 da suka kamu da cutar ta coronavirus, yayinda kuma annobar ta halaka wasu 977.

A matakin kasa da kasa, a yanzu haka annobar at COVID-19 ta kashe sama da mutane dubu 770, daga cikin sama da miliyan 21 da suka kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.