Najeriya

Najeriya: Darajar Naira ta rikito zuwa N480 kan dala daya

Takardun Naira dubu daya na Najeriya.
Takardun Naira dubu daya na Najeriya. Getty Images

Karfin kudin Najeriya na Naira ya kara raguwa da kashi 1 kan dalar Amurka a kasuwar canji ta bayan fage, inda a yanzu dalar 1 ke daidai da naira 480.

Talla

A kusan makwanni 2 da suka gabata dai darajar nairar ta tsaya ne kan 475 kan dala guda kafin samun koma bayan a jiya Talata.

A gefe guda kuma wasu na ganin bukatar dalar Amurkan da za ta karu la’akari da sake bude iyakokinta na sama ga jiragen saman kasa da kasa da Najeriya za ta yi a ranar 29 ga watan Agustan da muke, zai kara takura darajar naira da bankin kasar ya ragewa karfi har sau biyu a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.