Buhari-Wasanni

Buhari ya nada Amokachi matsayin mai taimaka masa kan wasanni

Tsohon tauraron kwallon Najeriya Daniel Amokachi.
Tsohon tauraron kwallon Najeriya Daniel Amokachi. CEOAfrica

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada tsohon tauraron kwallon kafar kasar Daniel Amokachi a matsayin mai taimaka masa kan harkokin wasanni.

Talla

Ministan wasannin kasar Sunday Dare ya sanar da nadin sakamakon wasikar da Sakataren Gwamnati Boss Mustapha ya rubuta wadda ta bayyana amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na baiwa Amokachi mukamin.

Wasikar da aka aikewa Amokachi ta ce shugaba Buhari na farin cikin sanar da shi nadin da aka masa na mai taimaka masa kan harkokin wasanni daga ranar 11 ga wannan wata na Agusta.

Daniel Amokachi na daga cikin fitattun 'yan kwallon kafar da suka daga darajar Najeriya wajen lashe mata kofin Afirka da Olympics, yayin da ya yiwa kungiyar Everton ta Ingila da Club Brugge ta Belgium da kuma Besiktas ta Turkiya wasa.

Sau 3 yana lashe kyauta dan wasan Afirka da yafi fice saboda kwarewar sa, yayin da ya taka rawa wajen kai Najeriya gasar cin kofin duniya na farko a Amurka da Faransa.

Tsohon dan wasan ya kuma lashe gasar cin kofin Afirka a matsayin mataimakin mai horar da ‘yan wasa, kana ya taba jagorancin kungiyar mata ‘yan kasa da shekaru 23.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.