Najeriya

'Yan siyasa sun maida hukumar NDDC na'urar ATM tsawon shekaru 19 - Akpabio

Ministan lura da yankin Niger Delta Sanata Godswill Akpabio
Ministan lura da yankin Niger Delta Sanata Godswill Akpabio The Guardian Nigeria / Twitter

Ministan lura da yankin Niger Delta Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana hukumar NDDC da aka dorawa alhakin raya yankin a matsayin na'urar ATM, da ‘yan siyasa ke tatsar kudin da suke kashewa wajen yakin neman zabe.

Talla

Ministan ya bayyana haka ne Yayin karbar bakuncin tawagar kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya IPMAN a birnin Abuja a karshen makon nan.

Sanata Akpabio yace matsalolin rashawa da almundahana sun dade da yiwa hukumar raya yankin na Niger Delta NDDC, katutu taswon akalla shekaru 19, Kafin nada shi Ministan lura da yankin a shekarar 2015.

Dan haka a cewar tsohon gwamnan na Akwa Ibom, kamata yayi majalisar dokokin Najeriya ta fadada binciken da take kan laifukan sace kudaden hukumar ta NDDC na tsawon shekaru 19 da yi da kafuwa, a mai makon zarge zargen almundahanar kudaden daga watan Fabarairu zuwa Yuli na shekarar 2020 da muke.

Ministan lura da yankin na Niger Delta, ya kara da cewar jumillar naira tiriliyan 5 gwamnati ta baiwa hukumar ta NDDC a tsawon shekaru 19, ba tare da an aiwatar da ayyukan da aka tsara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.