Najeriya

Najeriya na fuskantar koma bayan tattalin arziki mafi tsanani

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. Twitter/@BashirAhmad

Hukumar Kididdigar Najeriya ta sanar da cewar tattalin arzikin kasar ya samu koma bayan da ba a taba ganin irin sa ba a cikin shekaru 10 da suka gabata, sakamakon koma bayan da ya zarce sama da kashi 6 da aka gani tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni na wannan shekarar.

Talla

Alkaluman da Hukumar ta fitar yau sun nuna cewar tsakanin watannin Afrilu zuwa Yuni, sakamakon annobar COVID-19 da ta mamaye kasashen duniya da kuma dakatar da harkokin yau da kullum, tattalin arzikin Najeriya ya shiga yanayin da bai taba shiga ba tsakanin shekarar 2010 zuwa 2020.

Hukumar ta lissafa dalilan da suka haifar da matsalar da suka hada da tilastawa mutane zaman gida a fadin kasar da hana zirga zirgar ababan hawa da hana sufurin jiragen sama da rufe makarantu da kasuwanni.

Hukumar ta kara da cewar daukar irin wadannan matakai a kasashen duniya ya sa farashin man fetur ya fadi warwas, yayin da kuma aka rufe masana’antu a kasashen duniya domin tinkarar matsalar.

A watan Mayun da ya gabata, ministan kudin Najeriya Zainab Ahmed ta ce Hukumar Kididdigar ta yi hasashen fadawa cikin irin wannan yanayi, sakamakon wadannan matsaloli da suka hana gudanar da harkokin yau da kullum, abinda ya tilastawa gwamnatin kasar zabtare kasafin kudaden ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.