Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Alhaji Rabo Lawal kan arangamar jami'an tsaro da 'yan IPOB a Enugu

Sauti 03:33
Wasu 'yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra.
Wasu 'yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra. http://naijagists.com

Rundunar Tsaron farin kaya a Najeriya ta DSS ta ce masu fafutukar kafa kasar Biafra sun kashe jami’ansu 2 a arangamar da suka yi a Jihar Enugu, yayin da kungiyar ta ce jami’an tsaron sun kashe mata mutane 21.Ita ma kungiyar IPOB ta hannun kakakin ta Emma Powerful ta zargi jami’an tsaron Najeriya da kashe mata ‘ya'ya 21, inda ya ke cewa kungiyar su ta zaman lafiya ce.Dangane da wannan dambarwa Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Baturen 'yan sanda Alhaji Rabo Lawal, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.