MDD-Najeriya

MDD ta shawarci Buhari ya yi amfani da siyasa don magance matsalar tsaro

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ganawarsa da babban hafson Sojin kasar Laftanal Janar Buratai.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ganawarsa da babban hafson Sojin kasar Laftanal Janar Buratai. Solacebase

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi amfani da tattaunawa da kuma tafarkin siyasa wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

Talla

Babban Jakadan Majalisar da ke Najeriya Edward Kallon ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa fadar shugaban, inda ya ke cewa matsalolin tsaron da suka addabi kasar da ke da rassa daban daban na da wahalar magance su.

Kallon ya ce yayinda sojoji su ke can suna fafatawa, yana da matukar muhimmanci a goya musu baya wajen tattaunawa da amfani da hanyar siyasa domin samun zama lafiya.

Jami’in ya bayyana matsalolin da suka addabi Najeriya guda 3 da suka hada da matsalar zama dan kasa da mallakar dukiyar kasa da kuma rikicin shugabanci.

Kallon ya ce Majalisar na kashe akalla Dala biliyan guda da rabi kowacce shekara wajen gudanar da ayyukan jinkai a Najeriya, musamman a yankin da ake fama da rikicin boko haram.

Jami’in ya yabawa shugaba Buhari kan rawar da ya ke takawa wajen yaki da cin hanci da rashawa da kwato dukiyar jama’a tare da kuma sake fasalin ayyukan gwamnati, inda ya bukaci shugaban ya fadada wajen sanya hannu mazauna yankunan karkara cikin yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.