Kaduna

'Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai masu zana jarabawa a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai. REUTERS/Afolabi Sotunde

Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun farmaki wata makaranta tare da yin awon gaba da da dalibai 7 da malama guda baya ga kashe wani magidanci.

Talla

Majiyar da ke sanar da batun ta ce da misalin karfe 8 na safiyar jiya litinin ne ‘yan bindigar suka farmaki makarantar mai suna Prince Academy a kauyen Damba-Kasaya cikin karamar hukumar Chikun na jihar Kadunan lokacin da dalibai ‘yan aji 3 ke gab da fara zana jarabawa.

Jaridun Najeriya sun ruwaito cewa daliban na cikin wadanda gwamnatin Najeriya ta yi umarnin su koma makarantu don zana jarabawa.

Jaridun sun bayyana sunan malamar da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da ita a matsayin Christianah Madugu inda a bangare guda aka bayyana wanda ‘yan bindigar suka kashe a matsayin Benjamin Auta.

Wani matashi Akila Barde da ke shaidawa manema labarai yadda lamarin ya wakana ya ce ‘yan bindigar sun shiga kauyen ne haye a babura.

Bayanai sun ce ilahirin daliban shekarunsu ya fara daga 12 zuwa sama yayinda suka kunshi mata da maza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.