Najeriya-Kano

Ganduje ya amince da hukuncin kisa kan matashin da ya yi batanci ga Annabi

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Solacebase

A Najeriya Gwamnan jihar Kano da ke arewacin kasar, Abdullahi Umar Ganduje, ya sha alwashin zartas da hukuncin kisan da kotu ta yi wa matashin nan Sharif Aminu, matukar wa'adin da aka dibarwa matashin na daukaka kara ya kammala ba kuma tare da daukaka karar ba. 

Talla

Wannan matsaya ta gwamnan dai ta zo ne a dai dai lokacin matsin lamba ya yawaita kan gwamnatin jihar game da gaggauta amincewa da hukuncin.

To sai dai matukar wanda ake tuhumar ya daukaka karar kafin cikar wa'adin kwanaki 30 daga hukuncin kotun na farko, yazama wajibi a jira har zuwa kammaluwar matakan daukaka karar bisa tanadin dokar Najeriya

A ranar 10 ga watan Agustan nan ne babbar kotun musulunci da ke unguwar hausawa ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan Sharif Aminu bayan samunsa da laifin batanci ga Manzon Allah ''Annabi Muhammad tsira da Aminci su tabbata gateshi''.

Sai dai tuni kungiyoyin kare hakkin dan adam ciki har da Amnesty International suka shiga zancen tare da kalubalantar hukuncin kotun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.