Najeriya

Gwamnatin Najeriya za ta kashe dala biliyan 6 kan lantarki - Minista

Manyan turakun wutar lantarki a babbar tashar rarraba hasken lantarkin ta Azura-Edo dake birnin Benin City na jihar Edo a Najeriya. 13/6/2018.
Manyan turakun wutar lantarki a babbar tashar rarraba hasken lantarkin ta Azura-Edo dake birnin Benin City na jihar Edo a Najeriya. 13/6/2018. REUTERS/Akintunde Akinleye

Ministan lantarkin Najeriya Injiniya Sale Mamman, yace gwamnati ta ware dala biliyan 6 da miliyan 15, kwatankwacin naira tiriliyan 2 da biliyan 37, domin kawo karshen matsalar wutar lantarkin da kasar da share shekaru tana fama da ita.

Talla

Cikin sanarwar da ya fitar bayan cika shekara guda da nada shi kan mukamin, Ministan yace shirinsu a yanzu shi ne cimma matakin samar da lantarki da karfinta ya kai Megawatts dubu 25 nan da shekarar 2025 a karkashin yarjejeniyar aikin da Najeriya ta kulla da kamfanin Siemiens kan dala biliyan 2 da miliyan 300.

Wasu karin ayyukan da ministan lantarkin Najeriyar ya ce za a aiwatar da dalar biliyan 6 sun hada da gayara kananan tashoshin rarraba hasken lantarki 105 da gina wasu 70 sabbi, sai kuma samar da manyan layuka ko wayoyin lantarki na tsawon sama da kilomita dubu 5.

A halin yanzu dai karfin megawatts dubu 5 Najeriya ke da shi, da a wani lokacin ma kan sauka kasa da dubu 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.