Najeriya-Borno

Mayakan Boko Haram sun halaka dattijai 75 a Gwoza - Sanata Ndume

Wasu daga cikin al'ummar Gwoza dake jihar Borno masu gudun hijira a Adamawa, wadanda rikicin Boko Haram ya tilastawa tserewa daga muhallansu. 18/2/2014.
Wasu daga cikin al'ummar Gwoza dake jihar Borno masu gudun hijira a Adamawa, wadanda rikicin Boko Haram ya tilastawa tserewa daga muhallansu. 18/2/2014. REUTERS/Stringer

Dan Majalisar Dattawan Najeriya dake wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewar mayakan Boko Haram sun yiwa dattijan dake karamar hukumar Gwoza 75 yankan rago a dare guda.

Talla

Dan majalisar ya kara da cewar bayaga dattijan da suka halaka a watannin baya lokacin da suke kan ganiyar kaiwa hare-hare a sassan jihar Borno, mayakan na Boko Haram sun kuma yiwa matasa da dama kisan gilla a yankin na Gwoza, ta hanyar sanya su yin layi, inda suka kuma rika bi suna harbewa daya bayan daya.

Yayin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki da Majalisar ta shirya kan rikicin, a baya bayan nan, Sanata Ndume yace har ya zuwa wannan lokaci yankin sa na Gwoza na fama da matsalar tsaron da ba zai iya zuwa wurin ba.

Dan Majalisar wanda ya yabawa sojoji kan kokarin da suke, yace har yanzu rikicin Boko Haram bai kare ba, ganin yadda suke cigaba da hallaka mutane a Jiharsa.

Sanata Ndume ya kuma koka kan cewar har yanzu dubban al’ummar jihar Borno da sauran sassan yankin arewa maso gabashin Najeriya na fama da matsalar yunwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.