Najeriya ta sauya ranar dawo da zirga-zirgar jiragen sama zuwa ketare
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Najeriya ta sanar da dage fara zirga zirgar jiragen sama zuwa kasashen duniya da aka shirya farawa daga ranar 29 ga watan nan saboda karuwar masu kamuwa da cutar korona.
Ma’aikatar sufurin jiragen saman kasar ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin dakatar da fara zirga zirga saboda kar a bude kofa ga masu dauke da cutar daga kasashen duniya su dada yada ta.
Sanarwar ta ce za a jinkirta bude kofofin kasar zuwa ranar 5 ga watan Satumba.
Najeriya ta samu mutum na farko da ya kamu da cutar korona ne a watan Fabarairu lokacin da wani dan kasar Italia ya shiga da ita.
Ya zuwa yanzu wadanda suka kamu da cutar a Najeriya sun zarce dubu 50 yayin da sama da mutum dubu guda su ka mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu